Sudan ta Kudu

Sama da mutane dubu 300 sun hallaka a yakin Sudan ta Kudu

Wasu mayakan 'yan tawaye yayin shirin kaddamar da farmaki kan sojin Sudan ta Kudu, a wajen garin Kaya, dake kan iyaka da Uganda, ranar 26 ga watan Agusta, 2017.
Wasu mayakan 'yan tawaye yayin shirin kaddamar da farmaki kan sojin Sudan ta Kudu, a wajen garin Kaya, dake kan iyaka da Uganda, ranar 26 ga watan Agusta, 2017. REUTERS/Goran Tomasevic

Sakamakon wani bincike da aka gudanar kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu a yakin basasar kasar Sudan ta kudu da aka shafe shekaru 3 ana gwabzawa, ya nuna cewa dadadin wadanda suka hallaka ya kai dubu 383,000 ko sama da haka.

Talla

Makarantar koyar da ayyukan tsafta da kuma jami’ar koyar da aikin likita ta Tropicale dake birnin London na kasar Britaniya ne suka gudanar da binciken, wanda sai a ranar Talatar da ta gabata cibiyar dake kula da binciken samar da zaman lafiya ta Amurka ta wallafa shi.

Kwararrun da suka gudanar da binciken, sun kiyasta cewa mafi yawan adadin mamatan, an same shi ne kai tsaye a cikin fadace fadace, da kuma mace-macen da aka samu sakamakon cututtuka, da rashin tsafta tare da rashin samun tallafin magunguna ga marasa lafiyar.

A shekarar da ta gabata dai kiyasin da masu bincike suka fitar, ya nuna cewa adadin mutanen da suka hallaka a yakin basasar kasar ta sudan ta Kudu basu wuce dubu 100 da doriya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI