Nijar

Mutane 42 ne suka rasa rayukansu a Nijar

Wani yanki a jihar Damagaram da aka fuskanci ambaliyar ruwan sama
Wani yanki a jihar Damagaram da aka fuskanci ambaliyar ruwan sama ©RFI/David Baché

Hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta Ocha, ta ce akalla mutane 42 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu daminar bana a Jamhuriyar Nijar.

Talla

Alkalumman da hukumar ta Ocha ta dogara da su domin fitar da wannan rahoto, na nuni da cewa daga farkon daminar bana zuwa 16 ga wannan wata na satumab, mutane 42 ne suka rasa rayukansu, a wannan ambaliya da tuni ta raba shafi mutanen da adadinsu ya kai dubu 204 a sassan kasar.

Har ila yau rahoton ya cigaba da cewa gidaje dubu 16 da 992 ne suka rushe yayin da dabbobi manya da kanana sama da dubu 31 suka hallaka a daminar ta bana.

Ruwan sama mai karfin gaske, ya kuma haddasa ambaliya wadda ta share gonakin da fadinsu ya kai kadada dubu 7 da 579, inda manoma suka yi asarar abinda suka noma a wadannan gonaki baki dayansu.

Ambaliyar ta bana ta fi yin mummunan ta’adi ne a yankin Agadez da ke arewacin kasar da ba kasafai ake samun saukar ruwan sama a can ba, duk da cewa ta shafi wasu yankunan kudancin kasar da suka hada da Maradi da kuma Zinder, kamar dai yadda ambaliyar ta shafi biranen Yamai da kuma Tahoua a cewar rahoton na Ocha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.