Najeriya

An sanya dokar ta baci a jihar Filato dake Najeriya

Jami'an tsaro a wasu yankunan  da ake fuskantar matsalar tsaro a jihar Filato
Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a jihar Filato © AP

Gwamnatin Jihar Filato dake Najeriya ta kafa dokar hana fitar dare a kananan hukumomin Jos ta arewa da Jos ta Kudu bayan wani kazamin tashin hankali da aka samu wanda yayi sanadiyar rasa rayuka.

Talla

Rahotanni sun ce tashin hankalin ya biyo bayan kashe wani bafulatani da kuma daukar fan sa.

A yan watanni da suka gabata Shugaban Najeriya Muhammadu ya bada umurnin girke makaman atilare da jiragen sama da ke kai hari da kuma karin dakaru a yankunan da ake samun tashin hankali da ke Jihar Filato domin shawo kan matsalar da ta haifar da rasa dimbin rayuka.

Gwamna Lalon ya kuma bukaci kafa rundunar yan Sandan kwantar da tarzoma a Barikin Ladi domin kai daukin gaggawa wuraren da ake samun tashin hankali.

Mutane 11 ne suka rasa rayukan su a rikicin da ya kuno kai a jiya alhamis.

Bashir Ibrahim Idris ya hada rahoto a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.