Guinea Conakry

Shekaru 60 da Guinee Conakry ta samu yancin kai

Tsohon Shugaban kasar Guinne Conakry Ahmed Sékou Touré,
Tsohon Shugaban kasar Guinne Conakry Ahmed Sékou Touré, Dutch National Archives / CCAS 3.0

Yau shekaru 60 kenan da al’ummar Guinee Conakry suka kada kuri’ar neman ‘yancin kan kai, wadda sakamakonta ya baiwa kasar damar kasancewa ta farko da ta samu ‘yancin kanta daga Faransa a nahiyar Afirka.

Talla

Shugaba Ahmed Sekou Toure ne ya jagoranci bukukuwan samun ‘yancin kasar, to sai dai ‘yancin da al’ummar ta Guinee ta bukata, ya share fage ga sauran kasashe renon Faransa domin yin koyi da ita, to sai dai ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin kasar da kuma gwamnati Charles De Gaule da ke shugabancin Faransa a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.