Najeriya

Ministar mata a Najeriya ta yi murabus

Minitar dake kula da harkokin mata a Najeriya, Aisha Jummai Alhassan ta sanar da sauka daga mukamin ta, saboda abinda ta kira rashin adalcin da Jam’iyyar APC tayi mata wajen hana ta tsayawa takarar zaben Gwamna a zaben shekara mai zuwa.

Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya
Sanata Aisha Jummai Alhassan ta Jam'iyyar APC ta yi watsi da zaben Gwamnan Taraba a Najeriya REUTERS
Talla

A wasikar da ta rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kafofin yada labarai suka wallafa, tsohuwar ministar tace hana ta tsayawa takarar zaben babban rashin adalci ne a gare ta saboda ta biya kudin sayen takardar takarar kuma ta kwashe dogon lokaci tana biyayya ga jam’iyyar.

Jam’iyyar APC ta wallafa sunayen yan masu neman takarar gwamnonin jihohi ranar alhamis, inda ta bayyana Aisha Jummai Alhassan da Adebayo Shittu, ministocin Buhari guda biyu a matsayin wadanda suka kasa tsallake shingen tsayawa takarar.

Tsohuwar ministar ta dade ta na bayyana tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayin jagorar siyasar ta, amma kuma da ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar PDP sai taki bin sa.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda zata sanya gaba domin sake takarar kujerar gwamnan Taraba a zaben shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI