Chadi

Sojan Chadi sun murkushe yan Boko Haram a lardin tafkin Chadi

Tafkin Chadi
Tafkin Chadi SIA KAMBOU / AFP

Akalla mayakan Boko Haram 17 ne suka rasa rayukan su a wani tawo mu gama tsakanin dakarun Chadi da yan Boko Haram.

Talla

Rahotanni daga yankin tafkin Chadi na nuni cewa yan kungiyar Boko Haram su kai samame zuwa wasu wurare a kan iyaka da tafkin Chadi, inda aka samu gumurzu da dakarun Chadi.

Kanal Azem mai magana da yahun rundunar Chadi ya sheidawa kamfanin dilancin labaren Faransa cewa sojan Chadi sun samu nasarar kashe yan Boko Haram 17, yayinda mutane 6 da suka hada da soja daya, jami’in gandun daji daya da wasu farraren hula da harin ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.