Najeriya

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta janye yajin aiki

Ayuba Waba sakataren kungiyar kwadago na NLC
Ayuba Waba sakataren kungiyar kwadago na NLC

Kungiyar kwadago a Najeriya NLC ta sanar da janye yajin aikin da aka soma tun ranar alhamis na wannan makon.Kungiyar ta NLC ta tsuduma yajin aikin ne tareda bukatar mambobinta da sauran kungiyoyin da ke da nasaba da ita da su shiga gagarumin yajin aikin game-gari da ta kira.

Talla

Kungiyar ta NLC ta ce, ta kira yajin aikin ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza ci gaba da zaman tattaunawa game da amincewa da mafi karancin albashin ma’aikatan kasar.

Babbar kungiyar ta kwadago ta bukaci dukkanin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da bankuna da makarantu da gidajen man fetir da su koma ga aikin su kama daga gobe litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI