Najeriya

An tsamo motar Janar Alkali daga cikin tafki

Motar Janar Alkali
Motar Janar Alkali rfi hausa

Rundunar Sojin Najeriya bayan kwashe ruwan wani tafki da aka gano cewa an jefa gawar Janar Alkali da ake zargin an hallaka shi a wani yanki na Jihar Filato, ta yi nasarar tsamo motar janar din a cikin wannan tafkin.

Talla

Kisan babban hafsan sojin mai ritaya ya jefa fargaba ga mutane da dama a yankin, idan aka yi tuni a lokacin da hukumar bincinke ta sanar da yashe wannan tafki wasu mata sun yi zanga-zangar rashin amincewa da kwashe ruwan tafkin.

Ma su bincike za su mayar da hankali domin tanttance ma su hannu a wannan ta’adi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.