Isa ga babban shafi
Ghana

Melania Trump ta isa kasar Ghana

Matar  Donald Trump, Melania Trump da matar shugaban Ghana Rebecca Akufo-Addo a filin jiragen sama na Accra, Ghana Oktoba 2, 2018.
Matar Donald Trump, Melania Trump da matar shugaban Ghana Rebecca Akufo-Addo a filin jiragen sama na Accra, Ghana Oktoba 2, 2018. © AP
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
1 min

Matar shugaban Amurka Donald Trump ta isa birnin Accra na kasar Ghana a wannan talata, zangon farko a ziyarar da ta fara  a kasashe hudu na Afirka.

Talla

Dimbin jama’a ne a karkashin jagorancin matar shugaban kasar Ghana Rabecca Akufo-Addo suka tarbi Melania Trump lokacin da ta sauka a filin jiragen sama na Kotoka da ke birnin na Accra.

A lokacin wannan ziyara, bayan ganawa da matan shugabannin da za ta ziyarta, Melania za ta yi kokarin sanar da duniya wasu daga cikin muhimman ayyukan da hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID ke gudanarwar musamman a nahiyar ta Afirka.

Bayan kasar Ghana, matar shugaban na Amurka za ta kuma ziyarci kasashen Malawi, Kenya da kuma Masar karon farko tun lokacin  da mijinta ya dare shugabancin Amurka kusan shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.