Kamto yayi ikirarin lashe zaben Kamaru

Dan takara a zaben shugabancin Kamaru na jam’iyyar adawa ta MRC, Maurice Kamto, dake kan gaba tsakanin masu hamayya da shugaba mai ci Paul Biya, yayi ikirarin lashen zaben kasar da ya gudana a ranar Lahadi nan, 7 ga Oktoban, 2018.

Dan takara a zaben shugabancin Kamaru na jam’iyyar adawa ta MRC, Maurice Kamto.
Dan takara a zaben shugabancin Kamaru na jam’iyyar adawa ta MRC, Maurice Kamto. AFP/MARCO LONGARI
Talla

Kamto yayi ikirarin ne, duk da cewa ba’a kai ga kammala tattara sakamakon kuri’un da ‘yan kasar suka kada ba, zalika a gefe guda kuma akwai gargadin da gwamnatin kasar ta yi, kan hukunta wanda duk ya bayyana sakamakon zaben ba a hukumance ba.

A karkashin dokokin kasar Kamaru, bayan kammala tattara sakamakon kuri’un da aka kada, hukumar zaben kasar Elecam zata mika sakamakon karshen, zuwa kotun koli kasar, wadda ita ce mai alhakin bayyana shi, cikin kwanaki 15 bayan kammala zabe.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka samu kawance jam’iyyun FDP da MRC, irinsa na farko da aka taba gani a kasar tun bayan na shekarar 1992.

Jam’iyyun na FDP da MRC sun cimma yarjejeniyar ce, bayan da dan takarar FDP Akere Muna, ya amince da janye takararsa don marawa Maurice Kamto na MRC baya, domin kayarda shugaba mai ci Paul Biya, mai shekaru 85 dake neman zarcewa wa'adi na shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI