Wasanni

Senegal za ta karbi bakuncin gasar Olympics a 2022

Wasu daga cikin 'yan Senegal dake wakiltar kasar a wasannin motsa jiki.
Wasu daga cikin 'yan Senegal dake wakiltar kasar a wasannin motsa jiki. NBC Sports/Getty Images

Kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya, ya tabbatar da cewa Senegal ce za ta dauki nauyin shirya wasannin na Olympics na matasa da za a yi shekara ta 2022.

Talla

Kwamitin ya sanar da haka ne a zamansa karo na 133 da ya gudanar a wannan litinin a birnin Buenos Aires na kasar Argentina.

Senegal ta samu wannan nasara ce bayan doke kasashen Tunisia, Botswana da kuma Najeriya wadanda da fari, suka shiga sahun masu neman a basu wannan damar karbar bakuncin gasar Olympics din ta matasa a shekarar ta 2022.

Tuni shugaban Senegal Macky Sall ya bayyana gamsuwar al’ummar kasar dangane da wannan dama da aka basu.

Senegal ta kafa tarihin zama kasa ta farko daga nahiyar Afrika, da ta samu damar karbar bakuncin gasar ta matasan ta Olympics.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI