Bakonmu a Yau

Issa Tchiroma Bakary kakakin gwamnatin Kamaru kan zaben shugabancin kasar na ranar Lahadi

Sauti 02:53
Issa Tchiroma Bakary kakakin gwamnatin Kamaru.
Issa Tchiroma Bakary kakakin gwamnatin Kamaru. AFP/Pacome Pabandji

Yanzu haka ana cigaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar Kamaru, wanda aka gudanar a ranar lahadin da ta gabata, inda mutane 9 cikin har da shugaba mai ci Paul Biya suka kara da juna.Hukumar zaben kasar ta ce tabbas an samu karancin fitowar jama’a a lardunan da ke amfani da turancin Ingilishi sakamakon barazanar da ake fuskanta a bangaren tsaro, to amma duk da haka a cewar mahukuntan kasar zaben ya gudana a cikin kyakkyawan tsari.Wakilinmu na musamman Mahamman Salissou Hamissou wanda yanzu haka ke birnin Yaounde, ya zanta da ministan sadarwa sannan kuma kakakin gwamnatin kasar ta Kamaru Issa Tchiroma Bakary, domin jin yadda zaben ya gudana.