Najeriya

Ana zargin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci

Dr Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan jihar Kano
Dr Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan jihar Kano Daily Post

Kungiyar dake kare hakkokin yan Jaridu ta duniya dake da Cibiya a Amurka, wato CPJ, ta bayyana damuwar ta kan barazanar da Edita kuma mawallafin Jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ke fuskanta, sakamakon wallafa wani labari dake zargin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci daga yan kwangila.

Talla

Jami’an gwamnatin Jihar Kano suN musanta zargin da ake yiwa Gwamnan Umar Ganduje.

Jaafar Jaafar, ya sheidawa rediyo Faransa international RFI wasu daga cikin barazanar da yake fuskanta da kuma dalilin buyar da yake yanzu haka, .

Ana zargin wasu daga cikin jam’ian gwamnatin Najeriya da hannu a batutuwa da suka shafi cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.