Faransa-Rwanda

Batun kisan kiyashin Rwanda gaban kotun kasar Faransa

Tsohon shugaban Rwanda Juvénal Habyarimana a shekarar 1982
Tsohon shugaban Rwanda Juvénal Habyarimana a shekarar 1982 AFP

Masu shigar da kara a gaban kotun Faransa sun bukaci a jingine binciken da ake yi dangane da zargin kai hari a kan jirgin da ke dauke da shugaban Rwanda a 1994 Juvenal Babyarimana, wanda mutuwarsa ce ta haddasa barkewar kisan kiyashin da ya faru a kasar.

Talla

Bayan share tsawon shekaru ana gudanar da bincike, masu shigar da kara sun ce har yanzu an gaza gabatar da shaidar da ke tabbatar da cewa mutane7 da ake zare da su na da hannu wajen tarwatsa jirgin shugaban kasar, saboda haka ba hujjar cigaba da yin bincike a kansu.

Akalla mutane dubu 800 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin ‘yan Tutsi da ‘Yan Hutu bayan faruwar wannan lamari, wanda ya yi sanadiyyar tsamin dangantaka tsakanin Rwanda da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.