Jamhuriyar Congo-Ebola

Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Ma'ikatan lafiya a lardin Beni na Jamhuriyar Congo, Agusta 22, 2018.
Ma'ikatan lafiya a lardin Beni na Jamhuriyar Congo, Agusta 22, 2018. © AFP

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun ce annobar Ebola ta bulla a wani yanki na daban da ke gabashin kasar, bayan da aka yi shelar cewa an shawo kan cutar bayan da ta kashe mutane 125 a cikin watannin da suka gabata.

Talla

Ministan lafiyar kasar Oly Ilunga, ya ce annobar ta bulla ne a wani wuri da ke tsakiyar Beni, a lardin Kivu ta Arewa kusa da iyakar kasar da Uganda.

Ministan ya ce an samu bullar cutar a wannan yanki ne sakamakon yadda jama’a ke cigaba da bijire wa matakan mahukunta ke dauka domin hana yaduwar cutar ta Ebola

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.