Tanzania

Hukumomi na tsare da mutane 20 a Tanzania

Mohammed Dewji saman keke a Tanzania
Mohammed Dewji saman keke a Tanzania Mohammed dewji/twitter.com

A Tanzania hukumomin kasar sun sanar da capke mutane 20 da ake zaton suna da hannu wajen sace hamshakin mai kudin kasar Mohammed Dewji.Sanarwar da Ministan cikin gidan kasar Kangi Lugola ya bayar a wata ganawa da manema labarai ya jaddada cewa yan sanda na ci gaba da bincike don gano mutanen da suka kitsa wannan awon gaba.

Talla

Mohammed Dewji mai shekaru 43 ya kasance da mukamin dan majalisa kama daga shekara ta 2005 zuwa 2015,an bayyana dukiyar sa a Triliyan 1 da dugo 29 na euros.

Hukumomin Tanzania sun bayyana damuwa matuka bayan sace Mohammed Dewji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.