Libya-Rikici

An gano kabari dauke da gawarwaki sama da dari a Libya

Hafsan sojin Libya Khalifa Haftar (hagu) da shugaban gwamnatin Libya Fayez al-Sarraj
Hafsan sojin Libya Khalifa Haftar (hagu) da shugaban gwamnatin Libya Fayez al-Sarraj Fethi Belaid, Khalil Mazraawi/AFP

An gano wani makeken kabari dauke da gawarwarki sama da 100 kusa da birnin Syrte, daya daga cikin yankunan da ke karkashin ikon mayakan IS tun 2016.

Talla

A ranar laraba da ta gabata mahukunta a yankin na Syrte mai tazarar kilomita 450 daga Tripoli, sun ce an gano gawarwakin mutane 75 ne a wannan kabari, to sai dai an cigaba da bincike inda yanzu alkaluman ke cewa mamata 110 ne ke cikin wannan kabari.

Har ila yau an gano wasu kayayyyaki da ake jin cewa na wadanda aka kashen ne a cikin wannan kabari, da suka hada da wayoyin salula.

Gwamnatin Libya ta ce za ta gudanar da bincike a kan gawarwakin domin tantance su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.