Isa ga babban shafi
Habasha

An kama sojojin da suka yi kutse a ofishin Firaministan Habasha

Tutar kasar Habasha
Tutar kasar Habasha
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ce wasu sojoji da suka yi kutse a cikin ofishinsa cikin makon jiya, babbar manufarsu ita ce kawo cikas ga sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Talla

Da farko gwamnatin Habasha ta bayyana cewa a ranar 11 ga wannan wata na okotba ne wasu sojoji fiye da 10 suka yi kutse a cikin ofishin firaministan, inda da farko aka ce sun yi haka ne domin neman karin albashi.

A watan Yulin Shekarar bana ne Majalisar Habasha ta amince da shirin yi wa dubban ‘yan kasar Afuwa, wadanda a baya aka kama su da laifin tayar da rikici a sasan kasar.

Shirin afuwar ya shafi, mutane ko kungiyoyin da ake bincikarsu ko kuma aka yanke wa hukunci, bisa aikata laifukan cin amanar kasa, rashin mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ko kuma daukar makamai domin adawa da gwamnatin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.