Najeriya

Nnamdi Kanu ya bayyana bayan fiye da shekara guda

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB)Nnamdi Kanu.
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB)Nnamdi Kanu. STRINGER / AFP

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu da aka daina jin duriyarsa tsawon lokaci ya fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna shi yana ibada a birnin Qudus.

Talla

Faifan Bidiyo wanda Nnamdi Kanu ya fitar a yammacin jiya Juma’a, lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor ya tabbatar da cewa yanzu haka jagoran masu fafutukar na can yana ibada a birnin Qudus maimakon zargin da ake na kame shi a baya

Tun a watan Satumban 2017 ne aka rasa jin duriyar Nnamdi Kanu tun bayan wani sumame da dakarun soji suka kai gidansa da ke Abia a kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.