Kamaru-'Yan ware

'Yan bindiga sun sace dalibai 6 a yankin 'yan aware na Kamaru

Wasu jami'an soji lokacin da su ke rangadi a yankin 'yan awaren na Kasar Kamaru.
Wasu jami'an soji lokacin da su ke rangadi a yankin 'yan awaren na Kasar Kamaru. AFP

Wasu ‘yan bindiga a yankin ‘yan aware masu neman ballewa daga Kasar Kamaru sun yi garkuwa da dalibai 6 a makarantarsu da ke birnin bamenda na yankin arewa maso yammaci masu amfani da turancin Ingilishi.

Talla

Malamin makarantar da ya tsira da rayuwarsu daga hannun ‘yan bindigar ya ce tun da tsakar ranar jiya ne ‘yan bindigar suka isa makarantar tare da yin awon gaba da daliban 6.

Tun bayan komawa zangon karatu a watan Satumba ‘yan bindiga sun hallaka daraktan ilimi na yankin guda tare da kai mabanbantan hare-hare kan manyan makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.