Comoros

Ana ci gaba da tattaunawa da masu bore a tsibirin Comoros

Sojojin Comoros  a cikin  unguwar birnin Anjouan
Sojojin Comoros a cikin unguwar birnin Anjouan YOUSSOUF IBRAHIM / AFP

Dakarun tsibirin Comoros sun samu nasarar kutsa kai zuwa wasu yankunan unguwannin babban birnin kasar da ake zaton masu adawa da Shugaban kasar Azali Assoumani dauke da makamai ke buya.

Talla

Ministan ilimin kasar Mahamoud Salim Hafi ya sheidawa kamfanin dilanci labaren Faransa cewa sojoji sun yi nasarar shiga wasu daga unguwannin masu bore dake dauke da makamai, ba tareda sun muzgunawa mazauna wadanan wurare ba.

Ministan dake cikin tawagar da ta shiga tattaunawa da masu bore ya bayyana cewa duk da halin sulhu da aka cimma da masu bore ya zuwa yanzu ana sa ran za su mika makamai dake hannun su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.