Kamaru

Biya ya sake lashe zaben shugabancin Kamaru

Shugaban Kamaru Paul Biya ya lashe zaben da gagarumin rinjaye
Shugaban Kamaru Paul Biya ya lashe zaben da gagarumin rinjaye AFP

Shugaba Paul Biya da ya dare kan karagar Mulkin Kamaru tun shekarar 1982, ya sake lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye kamar yadda sakamakon da aka fitar a ranar Litinin ke nuna. Tuni gwamnati ta girke jami’an tsaro a babban birnin kasar, yayin da ake jin karar harbe-harben bindiga a yankin masu magana da Turanci Ingilishi mai fama da rikici.

Talla

Kotun Fasalta Kundin Tsarin Mulkin Kamaru da makusantan shugaba Biya suka mamaye ta, ta bayyana cewa, shugaban ya lashe zaben da kashi 71.3 na kuri’un da aka kada a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Shugaban Kotun, Clement Atangana, ya ce, babban dan adawar Biya a zaben, wato Maurice Kamto, shi ne ya yi na biyu da kashi 14.2 na kuri’un da aka kada.

Kotun ta samu kwanaki 15 bayan gudanar da zaben don sauraren korafe-korafen bayan zabe, in da ta yi watsi da dukkanin korafe-korafe 18 da aka shigar a gabanta, yayin da a yanzu babu wanda ya isa ya kalubalanci sakamakmon karshe.

Biya ya lashe zaben ne duk da zarge-zarge tafka magudi da karancin fitowar masu kada kuri’u har ma da barkewar rikici a yayin gudanar da zaben na Oktoba.

Jim kadan da bayyana sakamakon na yau, shaidu sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, ana ta harbe-harben bindiga a Buea, babban birnin yankin masu magana da Turancin Ingilishi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.