Najeriya

Kotu ta goyi bayan Najeriya kan wallafa sunayen barayin kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu tun bayan hawansa mulki ya sha alwashin bankado asirin wadanda suka yi watanda da kudaden lalitar kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu tun bayan hawansa mulki ya sha alwashin bankado asirin wadanda suka yi watanda da kudaden lalitar kasar. REUTERS/Darren Ornitz/File Photo

A Najeriya, babbar kotun kasar da ke zamanta a Abuja, ta goyi bayan matakin da gwamnati ta dauka, na wallafa sunayen wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa dama kwashe dukiyar al’umma da sauran laifukan almundahana.

Talla

A cewar kotun wallafa sunayen wadanda ake zargin da Ministan yada labaran Najeriyar ya yi cikin wannan shekara, bai tauye hakkin mutanen da ke cikin jerin masu laifin ba, zalika matakin ya na kan doka da oda.

Babbar kotun Najeriyar dai ta yanke hukunci ne kan karar da shugaban kafafen yada labaran AIT da Ray Power Cif Raymond Dokpesi ya shigar gabanta, inda ya ke neman kotun ta yi haramta matakin wallafa sunayen wasu mutane da ta yi a matsayin wadanda ta ke zargi da aikata laifukan almundahana, tare da neman a bi musu hakkinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.