Najeriya-Kaduna

An sassauta dokar takaita zirga-zirga a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai Daily Post

Gwamnatin Jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta sanar da sassauta dokar takaita zirga-zirgar da ta sanya a ciki da wajen birni daga awanni 24 na kowacce rana zuwa awanni 20 don bayar da dama da al’ummar jihar su gudanar da harkokinsu na kasuwanci.

Talla

Cikin sanarwar da babban mashawarcin Gwamnan Kadunan kan harkokin yada labarai Samuel Aruwan ya fitar yau Talata ya ce gwamnatin ta bayar da tsakanin karfe 1 na rana zuwa 5 na yamma ga al’umma don gudanar da harkokinsu.

Sai dai sanarwar ta ce sassaucin bai shafi al’umma unguwanni irinsu Kabala West da Kabalan Doki da Sabon Tasha da Narayi da Maraban Rido wadanda ya ce dukkaninsu dokar tana nan har awanni 24 kowacce rana.

Sanarwar ta Samuel Aruwan wadda ke shaida cewa matakin ya biyo bayan wani taron majalisar tsaron jihar a yau Talata, ya ce majalisar ta amince da janye dokar zuwa daga karfe daga kowacce karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.