Burundi-Tanzania

An fara taron sasanta bangarorin adawa a Burundi

Sai dai tattaunawar karkashin jagorancin Benjamin Mkapa, bai gayyaci gayyaci ‘yan adawa irinsu Jean Minani, shugaban majalisar sulhunta rikicin Burundin, a Arusha.
Sai dai tattaunawar karkashin jagorancin Benjamin Mkapa, bai gayyaci gayyaci ‘yan adawa irinsu Jean Minani, shugaban majalisar sulhunta rikicin Burundin, a Arusha. STR / AFP

An fara taron sasanta bangarorin siyasar Burundi a ciki da wajen kasar karo na biyar a birnin Arusha na kasar Tanzania.To sai dai ga alama za’ayi shi ne ba tare da bangaren gwamnati ba, domin kuwa jam’iyya mai mulki da kawayenta sun sanar da kaurace wa taron na yau.

Talla

A cewar kakakin gwamnatin Burundi Prosper Ntahorwamiye, a zantawarsa da sashin turanci na RFI, gwamnati baza ta shiga tattaunawar birnin Arusha ba sakamakon zaman makokin da za ta gudanar don tunawa da jaruman da suka kwanta dama a lokacin gwagwarmayar neman 'yancin kasar daga turawan mulkin mallaka.

Mista Ntahorwamiye, ya ce, masu shiga tsakanin basu mutunta bukatun da gwamnati ta tura musu kan jerin sunayen wadanda za a yi zaman tattaunawar da su ba.

Gwamnatin dai ta yi ikirarin cewa akwai wasu ‘yan adawa da bata bukatar duk wata nau’in tattaunawa da su, musamman wadanda ta ke nema ruwa a jallo don kama su.

Sai dai tattaunawar karkashin jagorancin Benjamin Mkapa, bai gayyaci gayyaci ‘yan adawa irinsu Jean Minani, shugaban majalisar sulhunta rikicin Burundin, a Arusha.

Haka zalika babu wani dan adawa da ke gudun hijira da aka gayyata a taron, abin da ya sa ma, babban sakataren wakilan ‘yan adawar da ke gudun hijira, Anicet Niyonkuru, ke ganin gwamnati na fakewa da zaman makokin don gujewa samar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.