Najeriya-Kano

An fara zaman sauraron bahasi kan bidiyon rashawar Ganduje a Kano

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje. Daily Post

A Najeriya yau ne aka fara zaman farko na kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa don bincikar faifan bidiyon nan da jaridar Dailly Nigeria ta wallafa da ke nuna gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hancin dala miliyan 5 daga hannun wasu 'yan kwangila.

Talla

Zaman na yau ya gudana ne karkashin kulawar fiye da kungiyoyin fararen hula 40, yayinda a bangaren guda farfajiyar majalisar ta cika makil da dai daikun mutane baya ga tarin 'yan jaridu da ke neman karin bayani.

Ka zalika jim kadan bayan zaman wanda Jafar Jafar Editan jaridar da gwamnatin Kanon ke zargi da yi mata gilli ya isa tun da wuri tare da tsayawa kan bakansa game da sahihancin bidiyon, wasu tarin kungiyoyi sun bayar da wa'adi ga Majalisar don yin hukuncin da ya dace.

An dai gudanar da zaman na yau ne bisa tsauraran matakan tsaro, baya ga tarin Dalibai da suka isa wajen inda suke nuna goyon bayansu ga Gwamnan kan cewa bidiyon fa ba zai hanasu zaben shi a 2019.

Sai dai tuni masharhanta suka fara diga ayar tambaya game da tarin daliban da suka halarci zaman na yau dama wadanda suka dauki nauyinsu ko kuma kitsa musu zuwa zaman Majalisar.

An fara zaman sauraron bahasi kan bidiyon rashawar Ganduje a Kano

Ga Karin bayani a rahoton da Abubakar Isah Dandago ya aiko mana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI