Najeriya-wasanni

Super Eagles ta dawo ta 3 wajen iya kwallo a Afrika

Jadawalin na FIFA dai ya nuna cewa yanzu Najeriya ita ce kasa ta uku mafi iya kwallo a nahiyar Afrika bayan kasashen Tunusia da Senegal.
Jadawalin na FIFA dai ya nuna cewa yanzu Najeriya ita ce kasa ta uku mafi iya kwallo a nahiyar Afrika bayan kasashen Tunusia da Senegal. Reuters/John Sibley

Kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta matsa gaba da mataki 4 a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya ke fitarwa duk wata kan kasashen da suka fi iya kwallo inda yanzu ta koma ta 44.

Talla

Cikin jadawalin da hukumar ta wallafa a shafinta yau Alhamis ya nuna cewa yanzu Najeriya na da maki 1431 a wanann watan fiye da na watan Satumba wanda ta ke da maki 1415.

Jadawalin na FIFA dai ya nuna cewa yanzu Najeriya ita ce kasa ta uku mafi iya kwallo a nahiyar Afrika bayan kasashen Tunusia da Senegal.

Ana dai ganin wanda dagawa da Super Eagles ta yi cikin sauri na da nasaba da nasararta kan Libya da ci 4 da banza a gida da kuma ci 3 da 2 a waje, yayin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Afrika.

Yanzu haka dai Tunisa ita ke matsayin ta 22 a Duniya sai Senegal a matsayin ta 24, yayinda kasashen Jamhuriyar Demokradoyyar Congo da Morocco ke matsayin na 46 da 47 cikin kasashe 50 mafiya iya kwallo a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.