Rwanda-Faransa

Sabon Bidiyo dangane da kisan Rwanda

Sabon Bidiyo dangane da kisan Rwanda
Sabon Bidiyo dangane da kisan Rwanda Capture d'écran vidéo Mediapart

Kafar yada labarai da ake kira Mediapart, ta fitar da wani hoton bidiyo a jiya alhamis da ke nuna babban hafsan rundunar sojin Faransa Kanal Jacques Rosier, na zantawa da wani karamin soji da ke karkashinsa na sanar da shi cewa a jiya sun ziyarci wani yanki da aka aiwatar da kisan kiyashin kasar Rwanda a shekarar 1994.

Talla

Har ila yau a cikin wannan hoton bidiyon wanda mallakin ma’aikatar tsaron Faransa ne, bayan da karamin sojin ya kammala yi masa bayani, Kanal Jacques Rosier ya karba masa tare da cewa ‘’na’am’’.

Ana jiran hukumomin Rwanda su bayar da Karin haske dangane da wannan hoton bidiyo,wanda ke nuna cewa dakarun Faransa na da labarin kisan jama`a a Rwanda.

Bayan share tsawon shekaru ana gudanar da bincike, masu shigar da kara sun ce har yanzu an gaza gabatar da shaidar da ke tabbatar da cewa mutane7 da ake tsare da su na da hannu wajen tarwatsa jirgin shugaban kasar na lokacin, saboda haka ba hujjar cigaba da yin bincike a kansu.

Akalla mutane dubu 800 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin ‘yan Tutsi da ‘Yan Hutu bayan faruwar wannan lamari, wanda ya yi sanadiyyar tsamin dangantaka tsakanin Rwanda da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.