Jamhuriyar Congo

'Yan adawa a Congo sun yi zanga-zanga ba tare da yamutsi ba

wasu daga cikin 'yan adawa da suka yi zanga-zangar neman soke matakin amfani da na'urorin zabe na zamani a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Congo.
wasu daga cikin 'yan adawa da suka yi zanga-zangar neman soke matakin amfani da na'urorin zabe na zamani a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Congo. AFP

Dubban ‘yan adawa a Jamhuriyar Congo, sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Kinshasa, ida suke neman tilastawa gwamnati soke na’urorin zabe na zamani, wanda aka shirya yin amfani da su, a zaben shugabancin kasar da zai gudana a watan Disamba mai zuwa.

Talla

‘Yan adawa a kasar dai na zargin cewa za’a yi amfani da na’urorin wajen tafka magudi a zabukan na watan Disamba, da suka hada dana shugaban kasa, da na ‘yan majalisu.

A wani yanayi na ba saban ba, shugaban kasar Joseph Kabila ne ya bada damar gudanar da zanga-zangar, wadda ta gudana ba tare da tashin hankali ba, sabanin yadda ake gani a baya, inda masu zanga-zangar ke arrangama da jami’an tsaron kasar.

Har yanzu al’ummar Jamhuriyar Congo basu yi sa’ar ganin bikin mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata ba cikin kwanciyar hankali, tun bayan samun ‘yancin kai daga Belgium a shekarar 1960.

Shugaba mai ciwa kuwa Joseph Kabila ya kasance bisa karagar mulki tun daga shekarar 2001.

Wa’adin karshe na mulkin Kabila ya kare ne, shekaru biyu da suka gabata, amma yaki sauka daga mulki, bisa dalilan rashin cikakken shirin gwamnatinsa na gudanar da sahihin zabe.

Daga bisani a watan da ya gabata Kabila ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba, matakin da wasu musamman ‘yan adawa ke ganin ba mai yiwuwa bane a baya, lamarin da ya haddasa gudanar da jerin zanga-zanga da tayi sanadin hallakar mutane da dama a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.