Mali

Masu tada kayar baya sun hallaka dakarun MINUSMA a sassan Mali

Motar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake sintiri a titunan garin Gao, dake gabashin kasar Mali cikin watan Agusta.
Motar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake sintiri a titunan garin Gao, dake gabashin kasar Mali cikin watan Agusta. AFP

Rundunar dakarun wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya, dake aiki Mali MINUSMA, ta ce 'yan ta-da-kayar baya sun hallaka biyu daga cikin jami’anta, tare da jikkata mata wasu da dama, a wasu tagwayen hare-hare 'yan bindigar suka kai a yankunan arewaci da tsakiyar kasar ta Mali a wannan Asabar.

Talla

Rundunar ta MINUSMA ta ce an kai harin farko kan sansaninta ne dake Ber a yankin Timbuktu, yayinda hari na biyu kuma masu tada kayar bayan suka kai kan sansaninta na Konna a yankin Mopti dake yankin tsakiyar kasar.

Dukkanin sojoji biyu da suka hallaka a hare-haren ‘yan kasar Burkina Faso ne, yayinda wasu dakarunta nata biyar suka jikkata.

Har yanzu dai akwai dakarun wanzar da zaman Lafiya na majalisar dinkin duniya akalla dubu 12,000 a Mali, karkashin rundunar MINUSMA, wandanda ke yakar mayakan kungiyoyi masu tattsauran ra’ayi.

A ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin Mali ta kara wa'adin dokar ta bacin da ta kafa da tsawon shekara guda. Dokar ta bacin dai ta baiwa jami'an tsaron kasar karin karfi wajen gudanar da ayyukansu na yakar ta'addanci da kuma baiwa alkalai ikon zartas da hukunci cikin gaggawa kan wadanda aka tabbatar da zargin alakarsu da ta'addanci.

Tun a watan Nuwamban shekarar 2015 gwamnatin Mali ta kafa dokar ta baci a kasar, bayan harin da aka kai kan babban Otal din dake birnin Bamako, inda mutane 20 suka hallaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.