Kamaru

An kashe Ba'amurken da ke wa'azi a Kamaru

Wani jami'in tsaron Kamaru a yankin masu magana da Turancin Ingilishi mai fama da rikici
Wani jami'in tsaron Kamaru a yankin masu magana da Turancin Ingilishi mai fama da rikici Reinnier KAZE/AFP

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, an kashe wani mai wa’azin addinin Kirista dan assalin kasar Amurka a Bambui, yankin da ke fama da rikicin ‘yan aware, bayan an bude wa motarsa wuta.

Talla

Majiya daga asibitin da aka kwantar da shi, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar, Ba’amurken ya mutu a ranar Talata da rana, sakamakon raunin da ya samu.

Yankuna biyu da ke amfani da Turancin Ingilishi sun tsindima cikin rikicin ‘yan aware, abin da ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.