Najeriya

An gano gawar bataccen sojin Najeriyar Manjo Janar Idris alkali

Motar Janar Alkali
Motar Janar Alkali rfi hausa

An tabbatar da gano gawar bataccen sojin Najeriyar nan Manjo Janar Idris alkali cikin wata tsohuwar rijiya da ake kira Guchwet da ke yankin Shen a karamar hukumar Jos ta kudu dake jihar Filato a Najeriya.

Talla

Da safiyar yau Laraba ne, aka kwashe ilahirin ruwan da ke cikin rijiyar aka kuma gano gawar babban jami’in sanye cikin wata jaka mai launin fari da kore.

Kafin yanzu dai rundunar sojin Najeriyar ta gano Motar Janar Alkali ne a cikin wani tafki da ke jihar ta Filato bayan umarnin yashe shi bisa rashin amincewar al’ummar yankin.

Majiyar sojin Najeriyar karkashin jagorancin Janar Umar Muhammad wanda na daga cikin wadanda aka dorawa alhakin lalubo wadanda ke da hannu a kisan ya ce sun gano rijiyar ne bayan shaida da suka samu daga guda cikin mutane 8 da ake zargi da kisan Manjon, wanda kuma shi ya mika kansa don amsa laifinsa.

Birgediya Janar Umar Muhammad ya ce mutane 6 yanzu haka na hannun jami’an ‘yan sanda yayinda ya bukaci sauran su mika kansu don gudanar da shari’a da rundunar sojin Najeriyar.

A cewarsa an gudanar da aikin gano gawar ne bisa hadin gwiwa tsakanin rundunar sojin da jami’an ‘yan sanda da kuma hukumar kashe gobara.

Tun a ranar 3 ga watan Satumban da ya gabata ne aka fara neman Janar Alkali wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja kuma aka daina samun wayarsa a dai dai lokacin da ya isa yankin kudancin Jos cikin motarsa mai lambar Kwara MUN 670 AA, yayinda aka gano motarsa ranar 29 ga wata a ranar juma’ar da ta gabata kuma rundunar ta ce ta gano wani kabari da ta ke kyautata zaton na Jami’in nata ne kafin gano shi a yau.

Tuni dai Rundunar ta dauke gawar Janar Alkali cikin wata motar Asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.