Wasanni

Kotu ta daure 'yan wasan Benin saboda karyar shekaru

Wasu daga cikin tawagar kwallon kafa ta kasar Benin, iyan kasa da shekaru 17.
Wasu daga cikin tawagar kwallon kafa ta kasar Benin, iyan kasa da shekaru 17. Starr Fm

Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta daure ‘yan wasan kwallon kafar kasar 10, dake cikin tawagar ‘yan kasa da shekaru 17, saboda samun su da laifin yin karya dangane da ainahin shekarunsu.

Talla

Kotun wadda ke zamanta a birnin Kotono, ta yankewa ‘yan wasan hukuncin daurin wata guda kowannensu.

Tun a watan Satumba aka kame ‘yan wasan dake ikirarin cewa ‘yan kasa da shekaru 17 ne, bayan bankado cewar karya ce kawai suka sharara, lamarin da yasa aka kore su daga cikin wasan neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika ta ‘yan kasa da shekaru 17.

Idan za’a iya tunawa a shekarar 2004, hukumar FIFA ta taba haramtawa Jamhuriyar Benin shiga wasanni saboda matsalolin cin hanci da rashawa da suka yiwa hukumar kwallon kafar kasar katutu.

Zalika tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013, hukumar ta FIFA ta sha yiwa kasar barazanar sake daukar matakin haramta mata shiga dukkanin wasanni, muddin ta gaza wajen gyara matsalolin da ke yiwa harkar kwallon kafa karan tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.