Sudan ta Kudu

Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu ya koma gida

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir daga bangaren hagu, tare da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar, bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya. (12/09/2018).
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir daga bangaren hagu, tare da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar, bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya. (12/09/2018). YONAS TADESSE / AFP

Madugun ‘yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya koma babban birnin kasar Juba, a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakaninsa da shugaban kasar Salva Kiir.

Talla

Karo na farko kenan da Machar, ya koma Sudan ta Kudu tun tserewar da yayi shekaru biyu da suka gabata, bayanda rikici ya sake barke tsakaninsa da shugaba Salva Kiir, wanda ya zarge shi da yukunkurin yi masa juyin mulki, lamarin da ya haifar da kazamin yaki tsakanin sojoji masu biyayya ga bangarorin biyu.

A wanna Laraba za’a yi bikin cimma sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, da kuma sake maida tsohon madugun ‘yan tawayen kan mukaminsa na mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir.

A cikin watan Agustan da ya gabata, Machar da ke fuskantar matsin lamba daga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma wasu kasashen Yamma, ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya da bangaren gwamnatin kasar bayan tabarbarewar yarjejeniyoyin farko.

A shekarar 2016 ne Machar ya tsere zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Congo mai makwabtaka da Sudan ta Kudu, kafin daga bisa ya isa Afrika ta Kudu, in da aka yi masa daurin talala har zuwa lokacin da aka fara wata sabuwar tattaunawa a watan Yuni.

Sudan ta Kudu da ta kasance jinjirar kasa a duniya, ta tsunduma cikin yakin basasa a karshen shekarar 2013, lokacin da dakaru masu goyon bayan shugaba Kiir suka yi artabu da dakarun da ke biyayya ga Machar.

Jim kadan da barkewar wannan rikici da ake dangantawa da na kabilanci ne, tashe-tashen hankula suka barke a sassan kasar, abin da ya kai ga rufe tashoshin hakar man fetir, yayin da miliyoyin mutane suka tsere daga kasar baya ga dubbai da suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.