Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta hallaka mutane 13 a kauyukan Borno

Shugaban Tsagin kungiyar Boko Haram Abu Musab Al-Barnawi mai biyayya ga reshen kungiyar IS.
Shugaban Tsagin kungiyar Boko Haram Abu Musab Al-Barnawi mai biyayya ga reshen kungiyar IS. Guardian Nigeria

Akalla mutane 13 ne ake fargabar sun mutu wasu da dama kuma su ka jikkata bayan hare-haren mayakan Boko haram cikin tsakaddaren jiya a wasu kauyuka 3 da kuma sansanin yan gudun hijira da ke Dalori 2 gab da birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Talla

Rahotanni na cewa, maharan sun kutsa cikin kauyukan Kofa da Bulabbrin baya ga wani bangare na sansanin 'yan gudun hijira na Dalori 2 tun da misalin karfe 7:50 na dare, inda suka yi ta barin wuta kan jama’a.

Kazalika mayakan sun kuma kona kauyukan kamar yadda wadanda suka shaida afkuwar lamarin suka tabbatar, sai dai babu rahoton ko mayakan sun yi garkuwa da jama'a.

A cewar rundunar ‘Yan Kato da Gora ta yi kokarin tunkarar mayakan amma suka fi karfinta la'akari da yadda suka kai hare-haren da manyan makamai.

Rahotanni sun ce kona gidajen da Boko Haram ta yi a kauyukan ya haddasa karuwar mutanen da suka rasa matsugunansu yayinda suma suka tare a sansanin 'yan gudun hijira na Dalori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.