Najeriya

Gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa kan karin albashi - Ngige

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar tattakin 'ya'yan kungiyar kwadago a garin Abuja. 20/06/2007.
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar tattakin 'ya'yan kungiyar kwadago a garin Abuja. 20/06/2007. REUTERS/Akintunde Akinleye

Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige, yace gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da bangaren kungiyar kwadagon kasar, don cimma matsaya kan bukatarsu ta neman karin mafi karancin albashin ma’aikata.

Talla

Ministan ya ce tattaunawar za ta gudana ne duk cewa a ranar Juma’ar da ta gabata, Kotun da ke shari’a kan rikicin masa’antu ta Najeriya ta yanke hukuncin haramta yajin aikin sai baba ta gani, da kungiyar kwadagon Najeriya ta kuduri aniyar somawa a ranar 6 ga watan Nuwamban da muke ciki, hukuncin da kungiyar kwadagon ta ce ba zai hana ta shiga yajin aikin ba.

Nigige ya kara da cewa a gobe litinin kuma, gwamnati za ta sake jagorantar wani zaman domin kawo karshen takkadamar da taki ci taki cinyewa.

Alwashin sake shiga yajin aikin da kungiyar kwadagon ta yi ya biyo bayan gaza amsa bukatarta da gwamnatin Najeriya hadi dana jihohin kasar suka yi na neman karin mafi karancin albashi daga naira dubu 18 zuwa naira dubu 30, inda gwamnatin tarayya ta yi tayin biyan naira dubu 24, su kuma gwamnoni suka yi tayin karin zuwa naira dubu 22 da 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.