Bakonmu a Yau

Karamin Ministan sufurin Najeriya Suleiman Hassan kan yadda ayyukan titunan kasar ke tafiyar hawainiya

Sauti 03:10
Kusan Ilahirin hanyoyin sufurin Najeriyar da ya kama daga na Mota da Jiragen kasa har ma da yankunan da mutane ke tafiya a kasa na bukatar gyara.
Kusan Ilahirin hanyoyin sufurin Najeriyar da ya kama daga na Mota da Jiragen kasa har ma da yankunan da mutane ke tafiya a kasa na bukatar gyara. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

A Najeriya, al'ummar kasar musamman a yankin arewaci na ta kokawa akan da-gwai-da-bayan da ake samu wajen gudanar da ayyukan shinfidawa da kuma gyara wasu Titunan kasar, hasali ma da yawa na cewar mahukuntan na nuna rashin kulawa ne saboda su a jirage su ke na su tafiye-tafiye.To sai dai da ya ke amsa tambayoyi dangane da hakan da Faruk Mohammad Yabo ya yi masa a Sokoto, karamin Ministan ayyuka da sufuri na kasar Sulaiman Hassan ya ce ba haka bane, ayyukan na tafiya kamar yanda ya kamata. Ga dai yadda tattaunawarsu ta kasance.