Cutar Ebola ta hallaka karin mutane a Congo
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ma’aikatar lafiyar Jamhuriyar Congo ta ce, yawan wadanda suka hallaka a dalilin cutar Ebola da ta sake bulla a kasar ya kai 201.
Kididdiga ta nuna cewa, rabin yawan mutanen da suka kamu da cutar mazauna garin Beni ne, dake lardin Kivu a gabashin kasar ta Jamhuriyar Congo.
Ministan lafiyar kasar Oly Ilunga Kalenga ya ce, tun bayan sake bullar cutar a watan Agusta an tabbatar da kamuwar mutane 319 a lardunan Kivu da Ituri, lamarin da yasa kasar ke fuskantar annobar cutar ta Ebola mafi muni a tarihinta, idan aka kwatanta da jimillar mutane 318 da aka kwatanta sun kamu da Ebolar a shekarar 1976, lokacin da ta soma bulla a garin Yambuku.
Karuwar yawan wadanda cutar Ebolan ta hallaka, ya zo ne a dai dai lokacin da jami’an lafiya ke gargadin cewa lamarin ka iya yin muni fie da halin da ake ciki, saboda hare-haren kungiyoyin ‘yan tawaye a yankunan da annobar cutar tafi shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu