Najeriya-EFCC

EFCC za ta dawo da Diezani Najeriya don fuskantar shari'a

Diezani Alison-Madueke tsohuwar ministar Albarkatun man fetur a Najeriya da ke fuskantar tuhmumar rashawa.
Diezani Alison-Madueke tsohuwar ministar Albarkatun man fetur a Najeriya da ke fuskantar tuhmumar rashawa. REUTERS/Rick Wilking/File photo

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta tababtar da cewar ta na kokarin dawo da tsohuwar minister fetur din kasar Diezaini Allison Madueke gida domin fuskantar tuhuma kan batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma halarta kudaden haramun.

Talla

Mai Magana da yawun hukumar, Tony Orilade ya ce sashen da ke kula da ayyuka na hukumar ya gabatar da bukata ga bangaren shari’a domin ganin ya dauki mataki akai.

Jami’in ya ce za’a dauki matakin ne ta ofishin ministan shari’a.

Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015, Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa da ya dabaibaye kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.