Najeriya-Kano

Ganduje na neman diyyar naira biliyan 3 daga Jaridar Daily Nigeria

Gwamnan ya kuma bukaci Jaridar ta biya shi diyya saboda abinda ya kira bata masa suna.
Gwamnan ya kuma bukaci Jaridar ta biya shi diyya saboda abinda ya kira bata masa suna. Daily Post

Gwamnan Jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya maka Jaridar Daily Nigerian a gaban kotu, saboda zargin da ta masa na karbar cin hanci daga ‘yan kwangila, inda ya ke bukatar dakatar da cigaba da wallafawa faifan bidiyon da kuma biyan sa diyyar naira biliyan 3.

Talla

Gurfanar da jaridar a kotu na zuwa ne wata guda bayan fara wallafa labarin da kuma sakin fafayen bidiyon.

Lauyan Ganduje, Nuraddeen Ayagi ya bukaci kotu ta dakatar da Jaridar daga cigaba da wallafa bidiyon da ta ce tana da shi wanda ke batawa gwamnan suna.

Gwamnan ya kuma bukaci Jaridar ta biya shi diyya saboda abinda ya kira bata masa suna.

Mawallafin Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar ya ce lauyoyin sa suna nazari kan karar kuma za su mayar da martanin da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.