Faransa

Morocco ta kaddamar da jirgin kasa na zamani mafi gudu

Bikin Kaddamar da layin jirgin kasa mai sauri na TGV a Morocco
Bikin Kaddamar da layin jirgin kasa mai sauri na TGV a Morocco ©RFI/Houda Ibrahim

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da sarki Mohammed na 6 na kasar Morocco a jiya alhamis sun kaddamar soma aikin jirgin kasar nan na zamani mai gudun gaske da zai hada biranen Tanger da Casablanca

Talla

Jirgin kasa na Morocco na a matsayin wanda ya fi ko wane jirgin kasa gudu a nahiyar Afrika, wata alama dake nuna irin ci gaba a hulda tsakanin biranen Paris da Rabat.

Sabon layin dogon mai sauri LGV zai fara jigilar fasinjoji a karshen wannan wata da muke ciki, inda zai dinga kai kawo a tsakanin biranen Tanger da Casablanca dake da tazarar kilomita 350.

Babu wata sanarwa a hukumance da shugabanin 2 suka yi sai dai sun nuna irin kusantar da suke da ita a lokacin kaddamar da aikin.

Tawagar jirgin ta cira ne a karkashin kwararan matakan tsaro kamar ko wacce tafiya da sarkin na Morocco ke yi kafin su isa a birnin Rabat a cikin awa daya da mituna 10 dake nuna dan tsaiko kadan a kan yadda aka zaci zuwansa a tasha

Kaddamar da layin jirgin kasar mai sauri na TGV na farko a Morocco da aka radawa suna "Al Boraq" da larabci ko kuma abin hawa, ya haifar da tsaiko ga tsarin kai kawon jiragen kasar kan babbar hanyar jirgi kamar yadda kafofin yada labarai suka sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.