Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Yan adawar Congo sun shiga tattaunwa a Belgium

Félix Tshisekedi da  Vital Kamerhe na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Félix Tshisekedi da Vital Kamerhe na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Photo-Montage/RFI/© AFP

Wakilan jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun cigaba da tattaunawa a birnin Brussels na kasar Belgium, domin dinke barakar da ta kunno kai a tsakaninsu dangane da tsayar da Martin Fayulu domin tsayawa takarar shugabacin kasar a zabe mai zuwa.

Talla

A cikin makon da ya gabata ne ,daukacin yan adawar suka rattaba hannu a yarjejeniyar tsayar da daya daga cikin yan adawa a matsayin dan takara,lamarain da ya harzuka Felix Tshisekedi da ya bukaci ficewa daga cikin kawancen yan adawar kasar.

‘Yan adawa da suka hada da Maurice Katumbi, Adolphe Muzito da kuma Martin Fayulu ne ke halartar tattaunwar, to sai dai jagoran daddiyar jam’iyyar adawar kasar Felix Tshisekedi da kuma Vital Kamerhe sun kaurace masa..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.