Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Kotu ta hana jaridar Daily Nigerian wallafa bidiyon rashawar Ganduje

Kafin yanzu dai Ganduje ya bukaci Kotun ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga bincike kan gaskiyar bidiyon amma majalisar ta ki amincewa.
Kafin yanzu dai Ganduje ya bukaci Kotun ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga bincike kan gaskiyar bidiyon amma majalisar ta ki amincewa. Solacebase
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Babbar kotun jihar Kano a tarayyar Najeriya ta umarci jaridar Daily Nigerian ta dakatar da wallafa bidiyon da ke nuna gwamnan jihar Abdullahi Ganduje na karbar cin hanci a hannun wasu ‘yan kwangila.

Talla

Hukuncin na yau litinin 19 ga watan Nuwamban 2018 karkashin mai shari’a Namallam na zuwa bayan karar da gwamnan na Kano ya shigar gaban kotun da ke neman ta haramtawa dan jarida Jafar Jafar ci gaba da wallafa bidiyon.

Mai shari’a Namallam ya bukaci Jaridar da mawallafinta su dakatar da duk wani yunkurin wallafa bidiyon wanda ya bayyana da bata sunan gwamnan Abdullahi Ganduje yayinda ya sanya ranar 6 ga watan Disamaban shekarar nan a matsayin ranar da za a dawo kotu don ci gaba da sauraron shari’a.

Kafin yanzu dai Ganduje ya bukaci Kotun ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga bincike kan gaskiyar bidiyon amma majalisar ta ki amincewa.

Wasu bayanai na nuni da cewa Gandujen na amfani da damar bayar da kwangila wajen karbar makuden kudade daga hannun mutane ko Kamfanonin da ya bai wa kwangilar a matsayin cin hanci ciki har da na Dala miliyan 5 da Jafar Jafar ya toni asiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.