Afrika

Taron koyar da dabarun yaki da ta addanci a Afirka

Mayakan Jihadi cikin garin Timbuktu na kasar Mali
Mayakan Jihadi cikin garin Timbuktu na kasar Mali AFP

Cibiyar dake kula da horar dabarun yaki da ayukan ta’addanci ta duniya (AILCT), da ya kamata ta kafa cibiyarta a birnin Abidjan na kasar Cote D’Ivoire a shekara 2019 na gudanar da wani zaman taron bita da ya samu halartar faransawa da dama da kuma wakilan yankin nahiyar Afrika.

Talla

A shekarar da ta gabata ne dai zaman taron kungiyar tarayyar turai da nahiyar Afrika da aka gudanar a birnin Abidjan ya bada shawarar kafa cibiyar da zata koyar da dabarun yakin da ta'addanci da kuma hana kwararar bakin haure zuwa nahiyar Turai.

Yankunan Sahel, arewacin Mali na daga cikin yankunan da yan ta’ada ke barrazana ga sha’anin tsaro.

A farkon  watan Nowemba ne kungiyar kakakin Majalisun dokokin kasashen Afrika a Najeriya da nufin samo sabbin dabarun da za a magance aikace aikacen ‘yan ta’adda da masu safarar kwayoyi da mutane a yankin ta gudanar da irin wannan taro a Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.