Abba Kiari Chetima kan yadda boko haram ta hallaka ma'aikatan Foraco 7 a garin Tumour na Jihar Diffa ta Nijar

Sauti 03:21
Jagoran tsagin kungiyar Boko Haram Habubakar Shekau.
Jagoran tsagin kungiyar Boko Haram Habubakar Shekau. News Ghana

Wasu yan bindiga da ake zato yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe wasu ma’aikata kamfanin Foraco 7 da ke aikin ginar rijiyoyin zamani a garin Tumour na jihar Diffa a jamhuriyar Nijar.Harin wanda 'yan kungiyar Boko Haram suka kai yau da asuba a garin na Tumour ya wakana ne a dai dai lokacin da jami’an tsaron da ke kula da kare lafiyar ma’aikantan kamfanin Foraco suka janye daga fadar magajin garin Tumour wurin da aka sauke ma’aikantan kamfanin na Foraco. Kan hakan ne kuma Abdoulaye Issa ya zanta da Abba Kiari Chetima, wani mazauni garin ga kuma yadda tattaunawar su ta kasance.