Alhaji Mohammed Uba Garba na hukumar hana fasakwauri ta kan iyaka da ke Seme kan kame haramtacciyar shinkafar da ake shirin shigar da ita Najeriya

Sauti 03:49
Najeriya dai ta haramta shigar mata da duk wata nau'in shinkafa bayan daukar matakin noma adadin shinkaafar da za ta iya ciyar da al'ummarta.
Najeriya dai ta haramta shigar mata da duk wata nau'in shinkafa bayan daukar matakin noma adadin shinkaafar da za ta iya ciyar da al'ummarta. The Guardian Nigeria

A Najeriya Hukumar hana fasakwauri da ke babbar kan iyakar kasar da Jamhuriyar Benin da ake kira mashigin Seme ta sanar da kame tarin haramtacciyar shinkafa da ake kokarin shigarwa Najeriyar daga ketare da kudinta ya tasamma biliyoyin naira.Alhaji Mohammed Uba Garba shine shugaban shiyyar Hukumar da ke Seme kuma ga abinda ya shaidawa Garba Aliyu Zaria.