Majalisar Najeriya na nazarin amincewa da sabbin Jami'o'i 80
Wallafawa ranar:
Majalisar Dokokin Najeriya na nazari kan shirin amincewa da sabbin jami’oi da manyan kwalejin fasaha da kwalejojin ilimi 80 domin wadata kasar da manyan makarantu.
Rahotanni sun ce yanzu haka aiki yayi nisa domin ganin an amince da wadannan bukatu da suk afito daga sassa daban daban na kasar.
Tuni kungiyar malaman jami’oi ta soki shirin, inda ta bukaci Majalisar da ta mayar da hankali wajen ganin an samarwa jami’oin da ake da su isassun kudaden aiki.
Sai dai wasu na ganin matakin zai taimaka wajen saukakawa miliyoyin dalibai samun guraben karatu a matakan gaba da sakandire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu