Boko Haram ta sace 'yammata 15 a Nijar
Wallafawa ranar:
Rahotani daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu mayakan boko haram sun sake kai hari garin Toumour da ke jihar Diffa a yammacin jiya tare da sace 'yammata akalla 15.
Wata majiya daga garin na Toumour da ta tabbatar da afkuwar lamarin ta ce ayarin mayakan su kusan 50 ne dauke da muggan makamai suka kaddamar da harin tare da yin awon gaba da 'yammatan.
Kawo yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna cewa sun kashe mutane kafin tafiya da 'yammatan 15.
Makamantan hare-haren na Boko Haram na ci gaba da tsananta a garin na Toumour inda ko a ranar alhamis din da ta gabata sai da mayakan na Boko Haram suka hallaka ma’aikatan wani kamfanin samar da ruwan sha na Foraco guda 8 da ke kan aiki a garin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu