Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Ebola

Jamhuriyar Congo ta amince da gwajin maganin Ebola kan jama'arta

Wannan dai ne karon farko da gwamnati ta amince da matakin tun bayan samar da maganin bayan karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar ta Ebola a fadin kasar.
Wannan dai ne karon farko da gwamnati ta amince da matakin tun bayan samar da maganin bayan karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar ta Ebola a fadin kasar. ®MSF
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Jamhuriyyar Dimokiradiyar Congo ta amince da yin gwajin maganin cutar Ebola kan wasu yan kasar da suka kamu da cutar, domin bai wa masanan kimiyya damar tattara bayanai game da sahihancin maganin.

Talla

Rahotanni sun ce tuni ma’aiakatan lafiya suka yi wa mutane sama da 150 gwajin maganin tun daga watan Agusta domin magance yaduwar cutar.

Ma’aikatar lafiyar kasar ta ce bayanan da za’a tatatra daga gwajin maganin zai ba da damar inganta shi domin ceto rayukan Bil Adama.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 228 suka mutu tun barkewar cutar watanni 6 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.