Uganda

Mutane 30 sun mutu bayan kifewar kwale-kwalensu a Uganda

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake fuskantar makamanciyar matsalar a kasar ta Uganda ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake fuskantar makamanciyar matsalar a kasar ta Uganda ba. REUTERS/Italian Navy/Handout via Reuters

Akalla mutane 30 suka mutu sakamakon kifewar da wani kwale kwale yayi dauke da mutane kusan 100 a cikin sa, lokacin da wasu masu bikin karshen shekara ke yawo a cikin tafkin Victoria a karshen wannan mako.

Talla

Kakakin 'yansanda Zura Ganyana ya ce sun yi nasarar ciro gawarwaki 30, yayin da aka ceto mutane 27 da ran su.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar ba’a kammala yi wa kwale kwalen garambawul ba, lokacin da matukan sa suka dibi mutane domin gudanar da bikin.

Daraktan Yan Sanda Asuman Mugenyi ya ce wani da ya tsallake rijiya da baya ya shaida masa cewar mutanen dake ciki sun zarce 90.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.